Ministan Ayyuka Ya Gargadi Kamfanonin Da Ke Aikin Titunan Tarayya Su Kammala Ko A Karbe Kwangilolin Su

Ministan ayyuka na Najeriya Sanata David Umahi, ya bukaci duk kamfanonin da aka baiwa kwangilar gina titunan tarayya, da su koma bakin aiki ko kuma a karbe kwangilolin daga hannayen su.

Ministan ya yi wannan jawabi ne yayin ganawa da kamfanonin da aka baiwa kwangilolin, inda yace gwamnatin tarayya a halin yanzu tana kokari ne wajen rage tarin basukan da suke kanta, sakamakon cire tallafi da kuma daidaita farashin kudi.

David Umahi yace akwai bukatar a bayar da cikakkun bayanai a kan kowane aiki, domin samar da ingantaccen tsari da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

Kazalika yace daukar matakin ya biyo bayan da kamfanonin suka bayyana cewa suna da isassun kudaden gudanar da ayyukan a lokacin da suka sanya hannu a kan kwangilolin.

Leave a Reply