Microsoft ba zai rufe ofishinsa na Lagos ba – gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotannin da kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka yaɗa da ke cewa, kamfanin Microsoft zai rufe reshensa da ke birnin Lagos wanda aka kafa domin amfanar da kasashen Afrika.
Babban Mai taimaka wa shugaban Najeriya a bangaren yada labarai, Temitope Ajayi ne ya fitar da sanarwar da ke musanta cewa, kamfanin na Microsoft na shirin ficewa daga ƙasar baki ɗaya.
Mista Ajayi ya ce, akwai kuskure a rahoton da kafafen yaɗa labaran suka fitar dangane da rufe ofishin na Microsoft, inda yake cewa, kamfani na samar da sauye-sauye a ayyukansa ne, amma ba wai shirin ficewa daga kasar ba.
A cewarsa, ma’aikata 30 ne kacal sabon sauyin na Microsoft zai taba, kuma ba wai za a sallame su daga bakin aiki ba ne, face sauya musu matsayi.

Leave a Reply