MDD ta yi tir da dokar Taliban da ta hana mata aiki a ƙungiyoyin agaji

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta yi tir da dokar da gwamnatin Taliban ta saka a Afghanistan wadda ta hana mata yin aiki a ƙungiyoyin agaji waɗanda ba na gwamnati ba.

Gwamnatin Taliban mai iƙirarin bin Shari’ar Musulunci ta kare matakin da cewa matan da ke aiki da ƙungiyoyin na karya doka ta hanyar ƙin saka hijabi.

Ta ɗauki matakin ne ‘yan kwanaki bayan ta hana mata ɗalibai zuwa jami’o’i.

Wasu mata ma’aikata sun Shaidawa BBC irin fargabar da suke da ita saboda su ne ke ɗawainiya da iyalansu.

Wata ta yi tambaya cewa: “Idan ban je aikina ba, wane ne zai kula da dangi na?”

Wata ma da ke ɗawainiya da iyalinta ta kira matakin da “mai rikitarwa” kuma ta haƙiƙance cewa ta bi dokar saka hijabin.

Leave a Reply