Mbappe ya yi yarjejeniya da Real Madrid, Arsenal ta samu damar sayen Onana

Sa’o’i 6 da suka wuce

Kylian Mbappe, ya cimma yarjejeniyar tafiya Real Madrid a ƙarshen kwantiraginsa da Paris St-Germain. (Foot Mercato)

Sai dai kuɗin da Madrid ɗin za ta biya Mbappe, wanda wa’adinsa a PSG zai ƙare a bazaran nan mai zuwa bai kai yawan wanda suka yi masa tayi ba a tattaunawarsu ta 2022. (Athletic)

Amma kuma duk da wannan yarjejeniya Mbappen zai iya sauya shawara ya tafi gasar Premier. (Times )

Juventus ta fice daga zawarcin ɗan wasan tsakiya na Manchester City Kalvin Phillips na Ingila saboda kuɗin da aka tsuga na bayar da shi aro da kuma yawan albashin da za a ba shi. (Fabrizio Romano)

Wannan janyewa da Juventus ta yi za ta iya ƙarfafa wa Newcastle damar samun ɗan wasan mai shekara 28. (Mail)

Liverpool za ta iya tsintar dami a kala idan Al-Ettifaq ta Saudiyya ta yanke shawarar sayar da ɗan wasanta na tsakiya Jordan Henderson na Ingila. (Mirror)

Everton ta sanya farashin fam miliyan 60 a kan Amadou Onana, wanda kuma ake ganin Arsenal na son sayen matashin ɗan wasan na tsakiya na Belgium mai shekara 22. (Football Insider)

Chelsea, da Manchester United da kuma AC Milan na sa ido a kan ɗan bayan Nice da Faransa Jean-Clair Todibo, amma kuma ƙungiyar ta Faransa na fatan riƙe shi a lokacin kasuwar ‘ƴan wasa ta watan nan na Janairu. (RMC Sport)

Wasu bayanai na cewa an bai wa Barcelona damar sayen tsohon ɗan wasan tsakiya na Manchester United da Ingila Jesse Lingard. Ɗan wasan mai shekara 31 ba shi da ƙungiya tun bayan da ya bar Nottingham Forest a ƙarshen kakar bara. (Sport)

Ɗan gaban Ingila Ivan Toney, ya ce yana da sauran aikin da yake so ya kammala yayin da yake shirin dawowa wasa a Brentford bayan dakatar da shi da aka yi tsawon wata takwas daga taka leda bayan saɓa dokokin caca. (Mirror)

Juventus za ta fara tattaunawa da ɗan wasanta na tsakiya Weston McKennie, Ba’amurke mai shekara 25 kan tsawaita kwantiraginsa. (Goal)

West Ham za ta nemi sayen ɗan bayan Wolves Max Kilman, ɗan Ingila idan ta samu kuɗi daga cinikin ɗan bayanta na Moroko Nayef Aguerd, a watan nan. (Guardian)

Ɗan wasan tsakiya na Newcastle Sean Longstaff ka iya barin ƙungiyar idan har aka samu ƙungiyar da ta saye shi da kima. (Sun)

Leave a Reply