Mbappe ya yi nadamar ƙin barin PSG, Real Madrid da Juventus na son Richarlison

Dan wasan gaba na Tottenham da Brazil Richarlison, mai shekara 25, ya shiga cikin jeren ‘yan wasa irinsu, Kylian Mbappe na Paris St-Germain da Faransa mai shekara 24, da Gonçalo Ramos na Benfica da Portugal, mai shekara 21, a matsayin wanda ake son su maye gurbin ɗan wasan Faransa Karim Benzema, mai shekara 35, a Real Madrid. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Juventus na kuma son ganin ta dauko Richarlison domin ya maye gurbin dan wasanta na Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 23, da ake sa rai zai bar kungiyar ta Serie A, a wannan kaka. (Calciomercato – in Italian)

Mbappe ya tuntubi Real Madrid a kakar da ta gabata – ta wakilansa – inda ya ce ya yi nadamar sabunta kwantiraginsa da PSG tare da bukatar kungiyar ta La Liga ta dauke shi. (Marca)

Real Madrid na son Mbappe, amma kuma fatansu shi ne su cimma yarjejeniya da shi idan kwantiraginsa na PSG ya kare a 2024. (AS – in Spanish)

Dan wasan Tottenham kuma kyeftin a Ingila Harry Kane, mai shekara 29, ya kasance wanda Manchester United ke hari a wannan kaka.

Amma dai Tottenham, a shirye su ke su bai wa Kane fifiko kan makomar kulob din inda suke kokarin ganin sun shawo kan sa, ya tsawaita zama da su bayan kwantiraginsa mai karewa a 2024.(90min)

Mai buga tsakiya a Manchester City da Jamus Ilkay Gundogan, dan shekara 32, ya kasance cikin ‘yan wasan da Barcelona ke hari a wannan kaka. (Sport – in Spanish)

Tsohon dan wasan Chelsea da Jamus Thomas Tuchel, mai shekara 49, ba zai yarda ya maye gurbin Antonio Conte ba a Tottenham muddin bai ga sun samu gurbi ba a kofin zakarun Turai. (Football Insider)

Inter Milan na nazarin dauko Conte, mai shekara 53, a matsayin kociya a karo na biyu yayinda suke shirin koran kocinsu Simone Inzaghi, mai shekara 46. (Football Insider)

Conte na iya barin Tottenham a karshen kaka da kuma maye gurbin Jose Mourinho na Portugal, mai shekara 60, a Roma. (Football Italia)

Dan wasan Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 28, ya yanke shawarar barin Inter Milan zuwa Paris St-Germain a wannan kaka. (Fabrizio Romano)

PSG tana da kasafin yuro miliyan 80 a wannan kaka, kuma za ta bukaci sayar da dan wasa guda tsakanin Neymar na Brazil mai shekara 31, da Lionel Messi na Argentina mai shekara 35, domin samun daman saye wasu sabbin ‘yan wasan. (Goal)

Inter Miami da wasu manyan kungiyoyi na amfani da duk wata dama na jawo hankalin Messi ya koma wasa a Amurka a wannan kaka.(L’Equipe – in French)

Brentford ba za ta sayar da mai tsaron ragarta ba David Raya, mai shekara 27, a wannan kaka in dai ba wai ta samu tayi mai gwabi ba ne duk da cewa tana Shirin barinsa ya tafi a 2024.(90min)

Nottingham Forest na iya sayen wasu sabbin ‘yan wasa a wannan kaka, yayinda ake Shirin bai wa kocinsu Steve Cooper kasafin sama da fam miliyan 100 indai suka dage basu fada a kasan teburi ba a Firimiya.(Football Insider)

Arsenal da Liverpool da Manchester United da Newcastle United na zawarcin dan wasan Kamaru mai buga tsakiya daga Lille Carlos Baleba, mai shekara 19. (90min)

Leave a Reply