Mazauna Amurka da Kanada na bikin Kirsimeti ba lantarki, cikin bala’in sanyi

Amurkawa da mazauna Kanada fiye da miliyan ɗaya ne ke bikin Kirsimeti cikin duhun ƙanƙara kuma ba tare da lantarki ba sakamakon tsananin sanyi da mummunar guguwa da ke addabar nahiyar Arewacin Amurka.

Mummunan yanayin ya jawo zubar dusar ƙanƙara, da iska mai ƙarfi, da kuma hunturu mai tsananin gaske.

Mutum kusan miliyan 250 lamarin ya shafa, kuma an samu rahoton mutuwar mutum 19 sakamakon guguwar mai nisan mil 2,000.

An soke dubban jirage na matafiyan da suka tsara tafiye-tafiyen Kirsimeti da sabuwar shekara.

Jihar Montana da ke yammacin ƙasar Amurka ce ta fi fuskantar matsalar, inda ma’aunin yanayi ya kai -50F (-45C).

Rahotanni na cewa kusan ba a iya ganin komai sai fari a jihohin Minnesota, da Iowa, da Wisconsin da kuma Michigan na Amurka.

A birnin Buffalo na Jihar New York kuwa, Hukumar Kula da Yanayi ta ce “ba a gane alamomin hanya a titi” wato zero-mile visibility a turance.

Leave a Reply