Mayakan Boko sun sake bankawa gidajen ‘yan gudun Hijra wuta a jihar Borno

  Wasu da ake kyautata zaton mayakan boko haram ne sun sake bankawa sabbin gidaje 25 da aka gina da niyyar sake tsugunar da ‘yan gudun hijra a karamr hukumar Dikwa dake jihar Borno.

A yanayi na zafafa kai hare-haren ‘yan tawaye, mazauna Dikwa sun bar gidajen su tare da zuwa su tare a sansanin tsugunar da ‘yan gudun hijra.

Wannan na zuwa ne bayan anyi garkuwa da wani dan gudun hijra lokacin da yaje daji domin samo itatuwan girki, inda mayakan boko haram suka karbe iko da kauyen Gajibo, bayan harbe-harbe babu kakkautawa da kuma bankawa sabbin gine-gine sama da 25 wuta.

A cewar wani shaidar gani da ido, Modu Kundiri, wanda ke kan hanyarsa Daga Maiduguri zuwa Gomboru, sun fuskanci tsayarwa daga dakarun soji na tsawon awanni 3 a kauyen Logonmani.

Wani mazaunin kauyen Dikwa, Sheriff Lawan ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawarsa da manaima labarai ta wayar tarho.

Gajibo gari ne mai tazarar kilometers daga Maiduguri babban birnin jihar.

Daga; Idris Usman Alhassan Rijiyar Lemo da Murtala Shehu Abubakar

Leave a Reply