Matatar man fetur ta Dangote za ta sayi ɗanyen mai ganga miliyan 24 daga Amurka

Matatar mai ta Dangote na shirin sayo aƙalla ganga miliyan 24 na ɗanyen man fetur daga Amurka nan da shekara mai zuwa domin ƙarfafa ayyukan matatar.
Cikin wani rahoto da jaridar Bloomberg ta fitar, ya nuna cewa matatar man fetur ɗin ta gabatar da buƙatarta na sayen ganga miliyan biyu a kowane wata daga kamfanin dillancin man fetur na ‘West Texas Intermediate Midland’ har na tsawon watanni 12 da za a fara daga watan Yuli, wanda hakan zai sa matatar ta sayi ganga miliyan 24 a tsowan shekarar.
Buƙatar neman man fetur daga Amurka na nuna irin fama da ƙarancin tono mai da Najeriya ke fama da shi, tare da nuna irin tasirin da matatar za ta yi a kasuwan man fetur ta duniya, da zarar ta fara aiki.
Najeriya dai ta kasa cimma kason da ƙungiyar OPEC ta ware mata na yawan man da za ta fitar na aƙalla shekara guda.

Leave a Reply