Rundunar yansandan kano ta tabbatar da kama wani matashi dan kimanin shekaru 26 mai suna Khalid Musa da wani takwaransa da yanzu yake kwance a gadan asibiti, bisa zarginsu da amfani makami wajen kwacen jaka a baburin adai daita sahu.
Matashin dan asalin unguwar sheka aci lafiya a yankin karamar hukumar Kumbotso sun fada hannun jami an yansandan ne da taimakon al ummar yankin ya faru.
Da yake yiwa wakilinmu a rundunonin tsaro Idris Uthman Alhassan Rijiyarlemo Karin haske jami in hulda da jama a na rundunar yansandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida masa cewa matasan sun shiga hannun jami ansu ne jimkadan da afkuwar lamarin a dai dai lokacin da mutunen yankin ke neman daukar dokar a hannu ta hanyar lakadawa matasan dukan kawo wuka.