Mataimakin gwamnan jihar Anambra Mista Nkem Okeke, ya sauya sheka daga Jam’iyyarsa ta APGA zuwa Jam’iyyar APC mai Mulkin kasa.
Ana ganin cewa sauya shekar da mataimakin gwamnan yayi na da nasa da rikice-rikcen da ya dabaibaye jam’iyyar ta APGA mai mulki a jihar ta Anambra kan wanda ya kamata yayiwa jam’iyyar mata takarar kujerar gwamna a zaben jihar da za’a gudanar a ranar 6 ga Watan Nuwamba.
Mista Okeke ya samu tarba ne daga shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban birnin tarayya Abuja, wanda ya samu rakiyar Shugaban jami’iyyar na ruko kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, da gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma wanda yake shugabantar kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar ta APC a zaben gwamnan jihar Anambra dake tafe.