Masu Gidajen Burodi Sun Janye Yajin Aikin Da Suka Tsunduma A Fadin Najeriya

Ƙungiyar masu gidajen burodi ta Najeriya ta bayyana cewa ta janye yajin aikin da ta shiga, bayan wata tattaunawa da ta gudanar da jami’an ma’aikatar noma ta ƙasar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta Mansur Umar, ƙungiyar ta ce ta cimma matsaya da gwamnatin Najeriya a tattaunawar tasu, wanda hakan ya sanya ta sanar da janye yajin aikin wanda ta fara a ranar Talata.

Daga cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙungiyar da gwamnati sun haɗa da fitar da metric tan 25,000 na alkama nan take ga kamfanonin fulawa domin sarrafawa da samar wa masu sana’ar burodi.

Haka kuma ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniya kan sake duba shirin samar da fulawa daga rogo da dankali da kuma dawa.

Sannan kuma an cimma yarjejeniyar tallafa wa masu sana’ar ta burodi ƙarƙashin wani shiri na ma’aikatar noma ta Najeriyar.

Leave a Reply