Masu barazanar hana zabe, cika baki ne kawai – Buratai

Tsohon Babban hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Burutai, ya bayyana kwarin gwiwa game da zaben Najeriya da za a fara a cikin watan Fabrairun 2023.

Janar Buratai, wanda dan kwamitin yakin neman zaben Cif Bola Ahmed Tinubu, ne na APC a zaben, yayin wata ziyara a sashen Hausa na BBC, ya ce yawancin masu barazanar hana zabe, magana ce kawai ta fatar baki , ba da gaske suke yi ba.

Ya ce “Ni a ganina barazana kawai suke, domin sojojin Najeriya da ‘yan sanda da ma sauran jami’an tsaro sun daura damarar tunkarar duk wanda zai tayar da wani hargitsi a lokacin zabe.”

Laftanar Janar Tukur Yusuf Burutai, ya ce akwai fargaba da koke koken da ake, a kan cewa za a iya samun matsala a lokacin zaben mai zuwa, to yakamata mutane su duba su gani a yanzu akwai ci gaba wajen tabbatar da tsaro a Najeriya, bisa la’akari da shekarun baya da aka yi zabe.

Buratai

“To idan har a baya a lokacin da ake fama da matsalar tabarbarewar tsaro an yi zabe lami lafiya, ina ga yanzu an samu ci gaba sosai wajen tabbatar da tsaro, don haka kowa ya kwantar da hankalinsa za a iya zabe mai zuwa cikin lumana da kwanciyar hankali, domin jami’an tsaro sun shirya,” in ji shi.

Tsohon Babban hafsan sojin kasa na Najeriyar, ya ce a yanzu akwai abubuwa biyu da yakamata ayi kafin lokacin zaben,

“Na daya shi ne jami’an tsaro da kuma gwamnati su fito su bayar da tabbaci a kan cewa za a dauki matakan da suka dace dai dai gwargwado, don ganin cewa an tabbatar da tsaro a lokacin zabe, in ji shi.

Laftanar Janar Tukur Yusuf Burutai, ya yi wannan jawabin ne a yayin da ya rage makonni a gudanar da babban zabe a Najeriya, kuma zaben ya zo ne a dai dai lokacin da ake fuskantar matsaloli da dama a kasar, da suka shafi tattalin arziki da kuma tsaro.

Hare haren da yan bindiga ke kai wa kan ofisoshin zabe musamman a jihohin kudu maso gabas, na daga cikin abubuwan da ake ganin za su iya kawo tarnaki a zaben da ke tafe.

To sai dai kuma duk da fargabar da ake nunawar, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya jadadda cewa zabukan za su gudana kamar yadda aka tsara.

Sannan ita ma hukumar zabe ta yi watsi da raɗe-raɗin da wasu bayanai da aka rinka yaɗawa kan yiwuwar dage zaɓen.

Leave a Reply