Masar ta yi kira ga ƙasashen duniya su cika alƙawuransu kan ɗumamar yanayi

A yayin da ake dab da buɗe taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara, mai masaukin baƙi wato ƙasar Masar ta yi kira ga ƙasashen duniya da su cika alƙawuran da suka ɗauka a baya.

Fiye da shugabannin duniya 120 ne ake sa ran za su yi jawabai a taron, wanda ake yi wa laƙabi da COP27, da za a gudanar a birnin Sharm el-Sheikh na ƙasar Masar

Ana sa ran halartar mutane kusan 40,000, to sai dai wasu masu rajin kare hakkin bil-adama ba za su halarci taron ba, saboda zargin da suke yi wa Masar na keta haƙkoƙin ɗan-adama.

Shugaban Taron kuma ministan harkokin wajen masar Sameh Shoukry ya yi kira ga shugabannin duniya da kada su bari matsalar ƙarancin abinci da makamashi da ke da alaƙa da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ya yi tasiri wajen ɗaukar matakan kare dumamar yanayi.

Leave a Reply