Manufofin Gwamnatin Tinubu Ne Silar Taɓarɓarewar Rayuwa A Najeriya —ACF

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa ta koka kan yadda wasu manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke haddasa taɓarɓarewar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin aikin yi a Najeriya.
ACF ta kuma yi gargaɗin cewa Najeriya na iya fuskantar ruɗanin zamantakewa, musamman a yankin Arewa idan ba a yi wani abu ba don magance taɓarɓarewar tattalin arziki.
Ƙungiyar ta ACF ta bayyana hakan ne bayan yin taron majalisar zartarwa ta ƙasa da ta gudanar a Kaduna.
A cikin sanarwar da kakakin ƙungiyar na ƙasa Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar kuma ya sanya wa hannu, ya koka da yadda matsalolin suka ci gaba da taɓarɓarewa a wasu wurare musamman a Arewa.
Ya ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arziki a kan cire tallafin man fetur, da kuma haraji da gwamnatin tarayya ta yi, yana mai cewa waɗannan manufofin ne ke haifar da raguwar walwalar yanayin rayuwar ’yan ƙasa.

Leave a Reply