Manchester United ta yaudareni – Cristiano Ronaldo

Dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo ya ce an yaudare shi a kungiyar, kuma baya ganin kimar Erik ten Hag, ana tilasta masa ya bar United.

An yi wa Ronaldo, mai shekara 37 alkawarin yana da rawar da zai taka a Old Trafford, bayan da bai samu barin kungiyar ba, wadda ta kasa samun gurbin Champions League kamar yadda ya yi fata.

Kyaftin din tawagar Portugal ya bayyana batutwa da dama a hirar da ya yi da Piers Morgan a shirin TalkTV.

An tuntubi United ko za ta ce wani abu kan zarge-zargen da Ronaldo ya yi.

Da aka tambayi Ronaldo ko mahukuntan kungiyar na son suga ya bar United, sai Ronaldo ya ce ”Haka ne, ba koci kadai ba har da wasu mutum biyu zuwa uku da suke da alaka da kungiya. An yaudare ni.”

Leave a Reply