Manchester City za ta fafata wasannin karshen kaka ba tare da mai tsaron raga Ederson ba

Ƙungiyar kwallon kafa ta Manchester City za ta fafata wasan ƙarshe na cin kofin FA da kuma wasan karshe na gasar Firimiyar Ingila ba tare da mai tsaron raga Ederson ba sakamakon raunin da ya samu a kusa da idonsa.
Ederson dan Brazil mai shekaru 30 ya samu raunin ne a minti na 69 na wasansu da Tottenham a Talatar da ta gabata, wanda ya tilasta maye gurbin sa da Stefan Ortega.
Jagorar ta Firimiya da ke fatan lashe kofin a bana na shirin haɗuwa da West Ham ne a ranar Lahadi, karawar da za ta bata damar ko dai lashe kofin karo na 4 a jere ko kuma kufcewar kofin dungurugum.
Kai tsaye idan kungiyar City ta yi canjaras a karawar a ɓangare guda Arsenal ta lashe dukkanin maki 3 na wasanta, kenan tawagar ta Mikel Arteta za ta tafi da kofin bisa banbancin ƙwallaye.

Leave a Reply