Man Utd za ta sayar da Sancho, Chelsea na son Mbappe

Manchester United na son sayar da dan wasanta na Ingila Jadon Sancho, to amma Aston Villa na son siyan dan wasan mai shekara 23 sai dai tana ganin ya yi mata tsada a fan miliyan 60. (Football Transfers)

Manchester United za ta kasance a gaba a kungiyoyin da ke son siyan dan wasan Faransa Kylian Mbappe mai shekaru 24 daga Paris st- German idan har Sheikh Jassim bin Hamad Al Thani, ya sayi kungiyar. (Metro)

Ana kyautata tsammanin Chelsea za ta nuna sha’awarta a kan Mbappe, bayan da dan wasan ya shaida wa kungiyarsa ta PSG cewa ba zai tsawaita kwantiraginsa ba bayan ya kare a 2024. (Times )

Real Madrid na kan gaba wajen zawarcin Mbappe a kakar bana, abin da zai ba wa Tottenham damar ci gaba da rike dan wasan Ingila Harry Kane mai shekara 29. (Mail)

Yayin da su kuma wakilan Kane, suka gana da jami’an PSG. (Mirror)

Arsenal ba ta da shirin ci gaba da amfani da dan wasanta da ta siya mafi tsada Nicolas Pepe dan Ivory Coast a kan fan miliyan 72, inda take son sayar da shi a bazarar nan. (Telegraph)

Kungiyar kwallon kafa ta Al-Hilal da ke Saudiyya ta taya dan wasan gaban Belgium a Chelsea, Romelu Lukaku, mai shekara 30, a kan fan miliyan 20 . (Guardian)

Aston Villa da Wolverhampton Wanderers na sha’awar dan wasan Borussia Monchengladbach mai shekara 22 Manu Kone wanda ake alakantawa da tafiya Liverpool. (Mail)

Tottenham ta kusa cimma yarjejeniya tsakaninta da mai tsaron ragar Brentford David Raya, mai shekara 27, sannan tana fatan daidaitawa a kan farashi mai rahusa da kungiyar, wadda ke son a biya ta fan miliyan 40 a kan dan wasan. (Standard)

Dan wasan Barcelona da kuma Sifaniya Jordi Alba, mai shekara 34, na tattaunawa da Inter Miami a kan shirin tafiya gasar ta Amurka. (Fabrizio Romano)

Barca na bibiyar dan wasan tsakiyar Sifaniya Alex Baena, wanda take son mayewa da dan wasan Manchester City IIkay Gundogan. . (ESPN)

Ita kuwa Coventry City ta nuna sha’awarta a kan dan wasan Chelsea Bashir Humphreys mai shekara 20. (Standard)

Leave a Reply