Man United ta ziyarci Forest a Carabao Cup ranar Laraba

Nottingham Forest za ta karbi bakuncin Manchester United a Carabao Cup zagayen daf da karshe da za su kara a City Ground ranar Laraba.

Kungiyoyin biyu sun fafata ranar 27 ga watan Disambar 2022 a gasar Premier League, inda United ta ci 3-0 a Old Trafford.

Wannan shi ne wasa na hudu da za su fuskanci juna a League Cup, inda United ta yi nasara a karawa uku baya.

United wadda ita kadai ce a Ingila ke buga League Cup da FA da Premier League da Europa League kawo yanzu na fatan daukar kofi ko kofuna a bana a karon farko.

Rabon da United ta lashe kofi tun bayan Europa Cup da ta dauka a 2017, bayan da ta doke Ajax karkashin Jose Mourinho.

United ta taba yin shekara shida ba ta dauki kofi ba a tsakanin 1977 zuwa 1983.

Kungiyar Old Trafford wadda ta ziyarci City Ground a karon farko tun bayan 1999 za ta buga wasan farko daga biyun da za su yi a Carabao a bana.

Casemiro ya gama hukuncin dakatarwa wasa daya, bayan karbar katin gargadi biyar a Premier, sai dai Anthony Martial da Diogo Dalot da kuma Jadon Sancho na jinya.

Mai tsaron ragar Forest, Dean Henderson na jinya, damar ba zai yi karawar ba, bayan da yake wasannin aro daga United.

Forest ta kai wasan karshe a kofin a 1992, amma United ta doke taa Wembley, sai dai kungiyar na kokari a yanzu haka, wadda ta yi rashin nasara biyu a karawa 11.

Leave a Reply