Man City ta hau teburin Premier bayan lallasa Southampton

Manchester City ta hau mataki na daya a kan teburin Premier League, bayan da ta doke Southampton 4-0 yau Asabar a filin wasa na Ethad.

City ta ci kwallo a minti na 20 da fara wasa ta hannun Joao Cancelo, minti 12 tsakani Phil Foden ya ci na biyu na biyar da ya zura a raga a kakar nan.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne City ta ci gaba da sanya kwallaye ta hannun Riyad Mahrez, sannan Erling Haaland ya kara kwallo ta hudu da ya zama kwallaye 15 da ya ci a bana.

Da wannan sakamakon Manchester City ta koma ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 23, bayan buga wasa tara.

Leave a Reply