MALLAM IBRAHIM KHALIL YACE GURGUWAR FAHIMTA AKAYI WA KALAMANSA

Fitaccen Malamin Addinin Islama Dan asalin Jihar Kano,  Malam Ibrahim Khalil, ya nesanta kansa da rubutun da wata kafar yada labaran kasa da kasa tayi na cewa rashin tuntubar majalisar malaman Jihar ne ya sanya gwamnatin ihar Kano yanke hukuncin bayar da damar gudanar da sallar Juma’a dana Idin karamar sallah a masarautu biyar dake fadin jihar Kano.

   Malamin ya barranta kansa da masu yin irin wadancan kalamai inda yace gurguwar fahimta ake yiwa wasu malaman su fadi fari ace baki suka fada.

 A yayin ganawarsa da shugaban sashin Addinin Musulumci na Tashar Guarantee Radio,  Mallam Usman Hamza Usman ta cikin wani shirin Addini mai suna ”Gwadaben Tsira”  da ya saba gayyato mashahuren malamai a ciki da wajen Kano.

 Malam Khalil ya ci gaba da cewa, duk wani abu da ya shafi mas’alar addini abune da baya son gaggawar zartar da hukunci na nan take, yana bukatar a tsaya a nazarceshi ta kowane bangare, domin a koda yaushe ita fahimta fuska ce.