MALAMAI SUN BUKACI A BUDE MASALLATAI A JIHAR KANO

Rahotanni sun ce wasu malaman addinin Musulunci sun bukaci gwamnatin jihar ta sake bude masallatan Juma’a domin a rika gudanar da salloli kamar yadda aka saba duk mako.

Rahotannin sun kara da cewa malaman sun bayyana haka ne a wata takarda da suka aike wa gwamnatin jihar.

Bukatar tasu tana zuwa ne a daidai lokacin da cutar korona take ci gaba da yaduwa a jihar ta Kano mafi yawan al’umma a Najeriya.

Ma’aikatar lafiya ta jihar ta tabbatar cewa mutum 707 ne jumulla suka kamu da cutar korona a Kano ya zuwa ranar Laraba da daddare.

Kazalika mutum 79 sun warke yayin da mutum 33 suka mutu.