Majalisar Wakilai Tace Hukumar Kula Da Jiragen Kasa Ta Najeriya Bata Samar Da Isassun Kudaden Shiga

Majalisar wakilai ta nuna damuwa kan yadda tace hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya bata samar da isassun kudaden shiga.

Wannan na zuwa ne bayan da ofishin akanta janar na kasa ya bayar da rahoton cewa daga watan Janairu zuwa Satumban 2023, Naira miliyan 345 kadai hukumar ta iya samarwa.

Majalisar tayi wannan koken ne a lokacin da babban daraktan hukumar kula da jiragen kasan Fidet Okhiria ya bayyana a gaban ta, yayin gabatar da bayanai kan kasafin kudin da za a kashe daga shekarar 2024 zuwa 2026 a babban birnin tarayya Abuja.

Fidet Okhiria yace na daga cikin kalubalen da suke fuskanta, yin aringizo wajen siyar da tikiti da wasu ma’aikatan hukumar ke yi, sai dai yace sun dauki matakan da suka dace kan wadanda aka samu da aikata laifuka da suka hadar dadakatarwa da ma kora baki daya.

Leave a Reply