Majalisar wakilan Najeriya ta umarci kwamitinta mai kula da hukumar gidajen yarin ƙasar ya gudanar da bincike kan yanayin da ake tsare mutane a Najeriya.
Shugaban marasa rinjaye a majalisar ne ya gabatar da wata buƙatar gaggawa inda ya nuna damuwa kan mummunan yanayin da ma’aikatan gidajen yari ke aiki, da kuma halin ƙunci da fursunoni ke ciki.
Honarabul Kabiru Alhassan Rurum ya shaidawa BBC cewa na dauki matakin ne domin yin gyara a harkokin da suka shafi gidajen kason, duba da yadda suke cunkushewa da marasa laifi.
Sannan ya ce akwai abin takaci ganin yadda ake cika fursunoni a daki guda, inda mutum 10 ya kamata su kwana sai ka an samu sama da mutum 50 a ciki.
Majalisar ta kuma kara da cewa, akwai bukatar tabbatar da za a maida gidajen yarin na gyaran hali, maimakon zamo wa wurin sake koyon lalata, sakamakon yadda ake gwamutsa masu kananan laifi da muggan laifuka.
”Yanayin da gidajen yari ke ciki da fursuna da ma’aikata abu ne da duk dan kasa na gari sai ya yi allawadai da shi, abubuwan da ke faruwa a gidajen yari a birni da kauye duk daya ne,” in ji Rurum.