Majalisar Dokokin Kano Zata Karfafa Samun  Walwalar Ma’aikatan Jaha

Majalisar Dokoki ta jahar kano ta bayyana cewa zata yi kokari wajen ganin  an karfafa walwalar ma’aikatan jahar, Duba da irin gudun mawar da ma’aikatan  suke bayar wa wajen cigaban jahar kano a tsawon shekaru.

Shugaban majalisar Dokokin Rt. Hon. Jibrin Ismail Falgore ya bayyana hakan a Wani sakon taya ma’aikatan jahar  bikin ranar ma’aikatan ta duniya,   wanda Sakataren yada labaran majalisar Kamaluddin Sani Shawai ya rabawa manema labarai, inda yace abin a Yaba wa ma’aikatan ne duba da jajircewar su wajen aiki,  duk kuwa da kalubalen da ake fuskanta na rayuwa.

Jibrin Falgore ya kara da cewa, akwai kyakkawan Shiri na  kyautata yanayin gudanar da aikin majalisar Dokoki ta yadda ma’aikatan zasu bada  gudun mawar da ya kamata don samun nasarar ayyukan Majalisar da ma jahar kano Baki daya

A madadin yan majalisar dokokin ta kano, Shugaban majalisar  yayi Fatan kammala bikin zagayowar ranar maaikatan ta bana  cikin Nasara.

Leave a Reply