MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KANO TA MUSANTA ZARGIN KARBAR NA GORO

Majalisar Dokoki ta Jihar kano ta musanta wani zargi da ke yawo a shafukan sadarwa wanda ke cewa yan majalisar sun karbi na GORO kafin su yi DOKAR rushe masarautun Jihar.
Cikin Wani bayani da Sakataren yada LABARAN majalisar Dokokin ta kano Kamaluddin Sani Shawai ya rabawa manema labarai kan batun, ya karyata zargi tare da cewa, batune da bashi da tushe bare makama.
Me magana da yawun majalisa Dokokin ta kano yayi Kira ga Jama’a kan suyi watsi da wannan magana, inda ya bukaci kafar yada LABARAN data wallafa zargin da cewa, ta nemi afwar majalisar Dokoki da Jama’ar kano nan da awa 24.
Wata kafar yada LABARAI a kano CE ta wallafa a shafin ta cewa, yan majalisar Dokokin sun karbi hancin motocin Hawa da kudi kafin su yi DOKAR rushe masarautun Jthar guda hudu

Leave a Reply