Majalisar dattawan kasar nan ta kammala karatu na 2 kan kudirin duba yuwuwar samarwa ‘yan kasar nan mazauna karkara guraben aiyukan dan fadada hanyoyin samar da kudaden shiga.
Sanata Muhammed Sani Musa dan jam’iyyar Apc daga Shiyyar Naija ta Gabas shine ya gabatar da kudirin a gaban zauren majalisar dattijai ta kasa, wanda akayiwa take da bada tabbacin samar da guraben aiyukan yi ga al’ummar karkara.
Sanata Musa daga cikin abunda dokar ta kunsa akwai duba yuwuwar tsare rayukan al’ummomin dake zaune a karkara ta hanyar ware ranaku kamar dari koyarda sana’o’i ga magidanci ko masu su koyi wani aiki bisa radin kansu.