Majalisar Ɗinkin Duniya ta nemi jin matsayin kotun duniya kan mamayen Isra’ila a Falasɗinu

Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya nemi jin matsayin shari’a daga babbar kotun duniya kan mamayen da Isra’ila ta yi wa yankunan Falasɗinawa.

Ƙudurin wanda ya samu goyon bayan ƙasa 87, sai 26 suka nuna adawa da shi ciki har da Amurka da Burtaniya.

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya tana da ƙarfin yanke hukunce-hukuncen da wajibi ne a yi musu biyayya, amma ba ta iya tilasta aiki da su.

Ƙuri’ar ta ranar Juma’a, ta zo ne kwana ɗaya bayan rantsar da Benjamin Netanyahu a matsayin firaminista na gwamnatin Isra’ila mafi tsaurin ra’ayi a tarihi.

Isra’ila ta mamaye Gaɓar Yamma da Kogin Jordan kuma ko da yake ta janye daga Gaza amma har yanzu Majalisar Ɗinkin Duniya tana kallon yankin a matsayin wanda ke ƙarƙashin mamaye.

Isra’ila na iƙirarin cewa gaba ɗayan Ƙudus ne babban birninta, yayin da Falasɗinawa ke cewa Gabashin Ƙudus ne babban birnin wata ƙasarsu da za a kafa nan gaba.

Amurka na cikin tsirarun ƙasashen da suka amince da Ƙudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

Leave a Reply