Mai alfarma sarkin Musulmi ya roki Malaman Jami’o’in Najeriya da kada su sake tsindima wani yajin aikin.

Mai alfarma sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli kan harkokin addinin musulunci ta kasa Alhaji Sa’ad Abubakar na uku, ya bukaci ‘ya’yan kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU da kada su sake tsindima wani yajin aikin sakamakon biyansu rabin albashi a watan da ya gabata.

Wanda hakan ya haifar rudani a reshan wasu jami’o’i mallakin gwamnati bisa manufar tsayawa kan kudirinsu na samar da cigaba.

A ranar Talata ne dai kungiyar Malaman jami’o’in reshan jihar Lagos UNILAG, dana jami’ar koyon ilimin aikin gona ta taraiya dake Abeokuta, suka shirya wata zaga zangar nuna adawa da tsarin da aka bi wajen biyansu albashin watan octoba.

Da yake jawabi yayin kaddamar da wasu rukunin dakunan karatu 25 da iyalan Babalakin, suka ginawa jami’ar Fountain dake Osogbo a jihar Osun, Sarkin Musulmin ya shawarci malaman da su samar da masalaha kan batun ta hanyar tattaunawa da gwamnati.   NL

Leave a Reply