Magoya bayan APC na gudanar da zanga-zanga a Kano

Daruruwan magoya bayan jam’iyyar APC ke gudanar da zanga-zangar lumana a ofishin hukumar zabe ta INEC da ke a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Masu zanga-zangar na buatar hukumar zaɓe ta sake nazari kan sakamakon zaben gwamnan jihar.

Hukumar zaɓen dai ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar adawa ta NNPP a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

Bayan doke babban abokin hamayyarsa Nasiru Yusf Gawuna na jam’iyyar APC mai mulkin jihar

Masu zanga-zangar sun ce kamata yayi a ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba

Jam’iyyar ta APC dai ta kuma miƙa wa hukumar INEC takardar ƙorafinta game da zaɓen

Leave a Reply