Madrid za ta dauki Bellingham, Burnley na hangen Carvalho

Real Madrid za ta dauki dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19 daga Borussia Dortmund kan kudi £87m da kuma karin wasu £21m. (Sunday Mirror)

Mutumin da ake sa ran shi ne zai zama sabon manajan Chelsea Mauricio Pochettino na so ya dubi kwarewar dan wasan Belgium Romelu Lukaku, wanda zai kammala wasan da ya ke yiwa Inter Milan a wannan kakar, to amma dan wasan mai shekara 30 ya na so ya yi zamansa a kungiyar kwallon kafan ta Italiya. (La Gazzetta dello Sport – in Italian)

Manajan Manchester United Erik ten Hag ya na sa ran dan wasan Ingila Marcus Rashford zai tsawaita kwantiraginsa da kungiyar ta Old Trafford, a yayinda da kwantiragin dan wasan mai shekara 25 na yanzu zai kare a karshen shekarar 2023-2024. (Viaplay, via Manchester Evening News)

Liverpool ta bukaci a rika sanarda ita hali da dan wasan tsakiya na Portugal Ruben Neves ya ke ciki a yayin da ya ke shiga watanni 12 na karewar kwantiraginsa da Wolves (Football Insider)

Aston Villa da Newcastle United da Tottenham da kuma Roma na sanya ido kan dan wasan gaba na kungiyar Wolves mai shekara 27 Hwang Hee-chan amma fa sai kungiyar ta sayar da wasu ‘yan wasanta kafun ta samu kudin sayansa a cewar (FFP). (Sunday Mirror)

Arsenal na duba yiwuwar sayen dan wasan Faransa mai shekara 22 Sacha Boey, wanda ya ke yiwa kungiyar kwallon kafar Turkiyya ta Galatasaray wasa. (Sunday Telegraph – subscription required)

Burnley tana hangen dan wasan Liverpool Fabio Carvalho kuma ta ce ko sayansa ko ma dai rancensa ne ta na so. (Football Insider)

Dan wasan Belgium Divock Origi ya shirya barin AC Milan a yayinda kungiyoyi a Turkiyya ke muradin dan wasan mai shekara 28, tsohon dan wasan na Liverpool ya fi so ya koma gasar Firimiya. (Il Corriere dello Sport, via Football Italia)

Brighton na tattaunawa dan dauko mai tsaron ragar Amurka Brian Schwake mai shekara 21 daga kungiyar Livingston a yayin da dan wasan Spaniya Robert Sanchez mai shekara 25 ke duba yiwuwar nausawa Seagulls. (Mail on Sunday)

Leave a Reply