Madrid ta ci buri kan Bellingham, Naby Keita zai bar Liverpool

Real Madrid ta ce hankalinta ya koma kacokan kan dan wasan tsakiyar Ingila da Borussia Dortmund, wato Jude Bellingham, kamar yadda jaridar Fichajes ta ruwaito.

Chelsea kuma ta mika tayinta na yuro miliyan 30, kan dan wasan gefen PSV Eindhoven, Noni Madueke, a cewar ESPN.

A wata mai kama da haka West Ham ta yi watsi da tayin Chelsea kan dan wasan gabanta, Michail Antonio, in ji Guardian.

Ita kuwa Barcelona ta ce ba matse take ta sayar da Memphis Depay ba, kuma tana farin cikin ci gaba da aiki da shi har zuwa sadda kwantiraginsa za ta kare a karshen kaka. (Athletic)

Sai kuma Everton da ke son sayen dan wasan gaban Manchester United, Antony Elanga. (Football Insider)

Anan kuma Liverpool ce ta kawo karshen tattaunawa da Naby Keita, wanda hakan ke nufin dan wasan zai bar kungiyar idan yarjejeniyarsa ta kare karshen kaka. (Football Insider)

Crystal Palace na fargabar mai tsaron bayan Manchester United, Aaron Wan-Bissaka ya mata tsada. (Sun).

Anan kuma Tottenham na shirin taya mai tsaron bayan Bayer Leverkusen da Ecuador, Piero Hincapie, fam miliyan 20.

Wolves na son sayen mai tsaron bayan Newcastle Jamaal Lascelles, idan suka kasa sayen Craig Dawson daga West Ham. (Football Insider)

Itama Nottingham Forest na dab da kammala cinikin dan wasan tsakiyar Palmeiras a Brazil, Danilo. (90min)

Sai kuma Bournemouth da ke shirin saka wa dan wasan Ghana Antoine Semenyo albashin fam 50,000 duk mako, don ganin ta raba shi da kungiyarsa Bristol. (Sun)

Leave a Reply