Ma’aikatan jinya na yajin aiki a Ingila da Wales da kuma Ireland ta Arewa

Dubban ma’aikatan jinya ne a Ingila da Wales da kuma Ireland ta Arewa ne suka shiga rana ta biyu da fara yajin aiki.

Ma’aikatan sun shiga yajin aikin ne saboda rashin biyan wasu hakkokinsu.

Yajin aikin shi ne na baya bayan nan da ma’aikata suka dauka a fadin Birtaniya saboda tsadar rayuwa.

Ma’aikatan hukumar kula da lafiya ta Birtaniya ne za su rinka kula da marasa lafiya a asibitoci saboda yajin aikin.

Kungiyar ma’aikatan jinyar ta ce duk da hahhawar farashin kayayyakin da ake samu a kasar, ba a kara musu kudi ba, kuma sun shan wuya wajen gudanar da aikinsu.

Gwamnatin kasar ta conservatin ta ce bukatar da kungiyar ta yi na bata karin kashi 19 cikin 100 ba zai yi wu ba.

Leave a Reply