Bayan da aka rufe saye da sayarwa ‘yan wasa a nahiyar turai, ‘yan wasan Najeria da dama sun samu komawa kungiyoyi daban daban a nahiyar ta turai da murza leda.
Dan wasa na baya bayannan shine tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Katsina United wato Samuel Noshiri, wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Real Oviedo dake kasar Spania dake buga karamar gasar wato(Segunda Division) a ranar laraba wanda ya sanya hannu na kwantiragin shekaru 2.
Babban labarin dake fitowa a yanzu shine, komawar kanin tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta KKano Pillars (Junior Lokosa) wato Anthony Lokosa.
Anthony Lokosa wanda ya buga wasanni a gasar premier league ta Nigeria ya koma karamar kungiyar kwallon kafa ta UD Almeria dake buga karamar gasa a kasar Spania (Segunda Division).
Anthony Lokosa me shekara 24 ya koma UD Almeria ne a matsayin aro da zabin kungiyar ta Almeria zata iya siyan sa daga kungiyar Pharco FC ta kasar Masar.