Liverpool ta kai wasan daf da karshe a gasar Zakarun Turai karo na 12, bayan da ta fitar da Benfica a wasannin bana.
Kungiyoyin sun tashi 3-3 a Anfield ranar Laraba, kuma Liverpool ta kai zagayen gaba da kwallo 6-4 gida da waje, bayan da ta yi nasara 3-1 ranar Talata a Portugal
Wadanda suka ci mata kwallayen a Portugal sun hada da Ibrahima Konate da Sadio Mane da kuma Luis Diaz.
Liverpool ta kai zagayen daf da karshe a ko dai Europa ko kuma Champions League karo na 12 kenan, bayan da take da Champions League guda shida jumulla.
Wannan shi ne wasa na 12 tsakanin kungiyoyin, kuma Benfica ta zama wadda Liverpool tafi haduwa da ita a gasar Turai, bayan da ta fuskanci Chelsea sau 11.
Liverpool ta yi nasara a kan Benfica sau bakwai, ita kuwa kungiyar Portugal ta ci hudu, wannan karon shi ne suka yi canjaras a tsakaninsu.
Da wannan sakamakon Liverpool za ta karbi bakuncin Villarael ranar 26 ga watan Afirilu, sannan ta ziyarci Sifaniya a wasa na biyu a daf da karshe a Sifaniya ranar 4 ga watan Mayu.