Liverpool ta hau kan teburin Premier League, bayan da ta doke Manchester United 4-0 ranar Talata a Anfield.
A minti na biyar da fara tamaula Liverpool ta ci kwallo ta hannun Luis Diaz daga baya Mohamed Salah ya kara na biyu a minti na 22, na farko da ya zura a raga tun bayan wasa uku a gasar.
Rabon da Salah ya ci kwallo tun ranar 12 ga watan Maris da Liverpool ta doke Brighton 2-0, shi ne ya ci na biyu a bugun fenariti.
Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Sadio Mane ya kara na uku, sannan Salah ya kara na hudu na kuma biyu da ya zura a raga a ranar ta Talata.
Kawo yanzu dan kwallon tawagar Masar ya ci 22 kenan a gasar Premier ta bana, shi ne ke kan gaba a yawan zura kwallaye a raga a kakar bana.
Da wannan sakamakon Liverpool ta hau kan teburin Premier a karon farko da tazarar maki biyu tsakaninta da Manchester City, wadda za ta yi wasa da Brighton ranar Laraba a Etihad, a wasan farko City ce ta yi nasara da ci 4-1.
A wasan farko da suka fafata a gasar ta Premier League da aka kara tsakanin kungiyar Anfield da Red Devils ranar Lahadi 24 ga watan Oktoba, Liverpool ce ta caskara United da ci 5-0 a Old Trafford.
Wadanda suka ci wa Liverpool kwallaye biyar a ranar sun hada da Naby Keita da Diogo Jota da kuma Mohamed Salah da ya zura uku rigis.
Liverpool wadda ke fatan lashe kofi hudu a bana ta kai wasan karshe a FA Cup, bayan da ta doke Manchester City 3-2 a wasan daf da karshe ranar Asabar.
Tuni dai Liverpool ta lashe Carabao Cup a kakar nan, za ta buga wasan karshe da Chelsea a FA Cup, itace ta daya a teburin Premier karon farko tun 5 ga watan Octoba.
Haka kuma Liverpool za ta kara da Villareal gida da waje a Champions League wasan daf da karshe.