Likitoci masu neman kwarewa sun shiga yajin aiki

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa wato Nigerian Association of Resident Doctors (NARD), ta sanar da fara yajin aikin gama-gari ba tare da kayyade lokacin karewa ba, bayan da gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar da sabon tsarin alawus dinsu.Sakataren kungiyar, Shuaibu Ibrahim, ne ya bayyana hakan bayan wani taron gaggawa na kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da aka gudanar ta yanar gizo a ranar Asabar.Ibrahim ya bayyana matakin gwamnatin a matsayin abin takaici, yana mai zargin cewa hakan ya tilasta likitoci komawa wani sabon yajin aiki.Ya ce kwamitin ya samu bayani kan shirin gwamnati na janye tsarin alawus din, wanda ya ce ya sabawa yarjejeniyar da aka cimma a baya tsakanin bangarorin biyu.Rikicin ya samo asali ne daga yarjejeniyar da aka kulla bayan wani dogon yajin aiki da likitocin suka yi a shekarar 2025, inda aka amince da inganta albashi da alawus-alawus, ciki har da na kiran gaggawa, aikin dare, aiki a karkara da kuma wasu ayyuka marasa nasaba da jinya kai tsaye.Ko da yake an tsara fara aiwatar da sabon tsarin ne a watan Janairu na 2026, daga baya aka mayar da shi zuwa Fabrairu, kungiyar ta ce yanzu gwamnati na shirin dakatar da shi gaba daya daga watan Afrilu.

Latest news
Related news

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here