Lauyoyi 191 Zasu Taimaka Wajen Yin Shari’a Kan Mutane Sama Da 1000 Da Aka Kama Da Aikata Laifukan Zabe

A kalla lauyoyi 191 da suka hadar da masu mukamin SAN ne zasu taimaka wajen gurfanarwa tare da tafiyar da shari’a kan mutane 1076 da aka kama da aikata laifukan zabe, wadanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gabatar.

Wadannan masu laifi dai an kama su ne a jihohi 35 dake Najeriya yayin gudanar da zabukan shekarar 2023 da suka gabata, inda jihar Ebonyi ta kasance wacce aka fi samun masu aikata laifin da a kalla mutane 216.

Idan dai za a iya tunawa, shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya Yakubu Maikyau SAN, yayin da ya kai ziyara hukumar zabe ta INEC, yayi alkawarin cewa kungiyar su za ta bada gudunmawa wajen daukar matakan da suka dace kan masu aikata laifukan zabe, domin tabbatar da bin doka da oda a Najeriya.

Ya kuma ce wannan wani yunkuri ne na hadaka daga hukumar zabe ta INEC, da kungiyar lauyoyi ta Najeriya har ma da rundunar ‘yansanda ta kasa wajen kawo karshen matsalar aikata laifukan zabe.

Leave a Reply