Lai Mohammed ya ce wa Atiku ya daina zargin Buhari kan batun Boko Haram

Ministan yada labarai da raya al’adu na kasar nan, Lai Mohammed, ya nemi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, da ya daina ɗora alhakin karuwar matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Atiku Abubakar ya bayyana mamakinsa kan yadda har yanzu ƙungiyar Boko Haram ke cigaba da cin karenta babu babakka, kamar yadda yake shaida hakan  a wajen wani yaƙin neman zaɓe a Abuja a ƙarshen makon da ya gabata. Lai  Mohammed ya ce kamata ya yi Atiku ya karkatar da akalar zarginsa kan jam’iyyar PDP duba da a lokacin ne kungiyar  ta boko haram ta bulla a Najeriya

Leave a Reply