Kwale-kwale Ya Yi Ajalin Dalibai 2 A Kano

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da nutsewar dalibai biyu na Kwalejin Aikin Gona ta Audu Bako da ke karamar hukumar Makoda a wani Dam.

Kakakin hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce lamarin ya rutsa ne dalibai uku, sai dai an ceto wani mai suna Ibrahim.

Abdullahi ya kara da cewa jami’an hukumar da masunta a yankin sun yi nasarar lalubo dalibai biyu; Abubakar Sanusi mai shekaru 22 da Salisu Ado mai shekaru 21.

Ya bayyana cewa da fari an ceto daliban a sume, amma daga baya likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

Abdullahi ya ce an kwantar da wanda ya kubuta a babban asibitin garin Danbatta, inda yake ci gaba da samun kulawar da ta dace.

Leave a Reply