Kungiyoyin Matasa Sun Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Sake Bude Iyakokin Kasa

Gamayyar kungiyoyin matasa na jihar Ogun sun yi kira ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya sake bude iyakokin kasa na kasar, domin a cewar su hakan zai kawo karshen wahalhalun da ‘yan Najeriya suke fuskanta.

Matasan dai sun bayyana damuwar su da cewa duk matakan da gwamnatin tarayya take dauka domin kawo sauki basa isa ga matasa musamman wadanda ke fama da rashin ayyukan yi.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abeokuta babban birnin jihar Ogun, mai magana da yawun wannan gamayya Femi Owoeye ya jaddada muhimmancin da bude iyakokin ke da shi wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Kazalika yace idan har gwamnati ta dauki matakin zai taimaka wajen dakile hauhawar farashin kayayyakin masarufi musamman ma na abinci.

Kazalika sun bayyana hanyoyin da ya kamata a ce gwamnatin ta bi wajen kaddamar da ayyukan ta, da suka hada da samar da ayyukan yi ga matasa, bayar da tallafi ga masu kananan sana’o’i da ma baiwa matasa damarmaki a tsarin tafiyar da gwamnati.

Leave a Reply