Kungiyoyi masu zaman kansu na da rawar takawa a fagen cigaban wasanni – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari yayi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu dasu bada gudunmuwa domin cigaban wasanni a fadin tarayyar kasarnan.

Buhari yayi wannan kiran ne yayin bikin bude gasar wasanni ta kasa karo na ashirin da daya a birnin Asaba dake jihar Delta.

Shugaba Buhari ya samu wakilcin shugaban ma’aikatar matasa da wasanni ta kasa Mista Sunday Dare yayin bikin bude gasar.

Shugaban ya bayyana cewa, gasar wasanni ta kasa wata gaba ce dake zakulo matasan yan wasanni tun daga tushe.

Ya kara da cewa, gasar wasannin ya zakulo yan wasanni da suka wakilci Najeriya a gasanni daban-daban kamar su gasar wasannin nahiyar Afrika, gasar guje guje da tsalle tsalle da kuma gasar wasannin rainon kasashen ingila.
Buhari ya kuma gode tare da jinjinawa jihar Delta data cika alkawarin karbar bakuncin gasar.

A nashi bangaren, gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa ya tura sakon maraba ga yan wasanni da suka fito daga jihohi 36 dake fadin kasar nan hadi da babbar birnin tarayya Abuja.

Okowa ya kara da cewa, yana sa rai jihar Delta ce zata kare matsayin ta na farko kaman yadda tayi karo na ashirin a jihar Edo.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin bude gasar akwai gwamman jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal dana Edo Godwin Obaseki.

Leave a Reply