Kungiyar wakilan kafafen yada labarai masu aikewa da rahotanni reshen jihar Kano, ta ce ta kauracewa dukkanin wasu harkoki na gwamnatin Kano, nan take.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da shugaban kungiyar Aminu Ahmed Garko ya sanyawa hannu a litinin din nan.

Garko ya bayyana kyara, cin mutunci da tsangwama da ya ce wakilan nasu na fuskanta daga gwamnati da wakilanta yayin gudanar da aiyukansu a fadin jihar.

Kazalika kungiyar ta koka kan yadda ta ce, gwamnatin na amfani da wadanda ba ‘yan yaridu ba wajen daukar harkokin gwamnati, maimakon barin ‘ yan jaridu su yi aikinsu bisa kwarewa.

A Saboda haka ne kungiyar ta ce daga yanzu ba zata sake halartar taron yan jaridu, ko wata ganawa da wakilan gwamnati ba, har sai an samu gyara kan ‘yanci da kuma kare lafiyar yan jaridu a fadin jihar.

Leave a Reply