Kungiyar Tarayyar Turai, ta yi tir da Allah wadai da yadda mahukuntan kasar Chadi suka hana masu sanya idanu kan zaben kasar kusan dubu 3 gudanar da aikin su yadda ya dace.

Mafi yawan masu sanya idanun da aka hana gudanar da aiki yadda ya dace na cikin tawagar da EU din ta dauki nauyi.

Tuni dai yan adawa suka bukaci a kauracewa zaben a cewar su an tafka manyan kura kurai da kuma tafka magudi.

Suma dai kungiyoyin da suka shiga kasar don sanya idanu game da zaben sun ayyana shi a matsayin wanda ke cike da kura-kurai ganin yadda gwamnati ta gaza yin komai da ya shafi zaben a bayyane.

Leave a Reply