Kungiyar Mata Manoma sun tafka asarar naira milyan 200 a  Nassarawa.

Kungiyar mata manoma wadanda galibi, su ke samar da abinci a jihar Nassarawa sun ce ambaliyar ruwa ta lalata amfanin gonarsu na kimanin  naira milyan 200 a kananan hukumomi 13 dake fadin jihar.

Galibi matan sun yi korafin cewa sun tafka asarar ne sakamakon yawaitar ambaliyar ruwa wanda hakan ya jefe su cikin wani mawuyacin hali! Kazalika sun yi fargabar cewa hakan ka iya shafar rayuwar iyalansu idan har ba’a kawo musu dauki ba.

Guda daga cikin shugabannin kanana da matsakaitan manoma a jihar Mrs. Justina Anjugu, ta ce a iya karamar hukumar Lafiya dake jihar ta Nassarawa, mata sama da 500 ne suka tafka asara a gonakinsu na kimanin naira milyan 50 sakamakon ambaliyar ruwa!

A cewar ta yankunan da lamarin ya fi kamari sun hadar da Loko, Doma da kuma Tunga, inda mata da yawa suka rasa amfanin gonar su a ambaliyar ruwan.

Leave a Reply