Kungiyar Masu Masana’antu Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Tallafawa Masu Samar Da Kayayyaki a Cikin Gida

Kungiyar masu masana’antu ta Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta dinga tallafawa masu samar da kayayyaki a cikin gida domin habaka tattalin arzikin kasar, da kuma farfado da darajar Naira a kasuwar hada hadar kudade ta duniya.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar ta yaba da kokarin shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da cigaba a fannin tattalin arziki musamman a shiyyar Kudu maso Gabashin kasar, karkashin shirin samar da ci gaba na ‘Light-up Nigeria’.

Da take bayani a wajen taron kaddamar da shirin a jihar Enugu, shugabar kungiyar ta jihar Lady Ada Chukwudozie, tace muddin gwamnati ta tallafawa masu samar da kayayyaki a cikin gida, darajar Naira za ta dago kuma za a samar da ayyukan yi ga matasan Najeriya.

Leave a Reply