Kungiyar Kwadago Ta NLC Za Ta Nemi Mafi Karancin Albashin Naira Miliyan Daya A Najeriya

Kungiyar kwadago ta NLC ta bayyana cewa idan har tsadar rayuwar ake fama da ita a Najeriya ta ci gaba, to tabbas babu zabin da ya wuce su mika bukatar neman naira miliyan guda a matsayin mafi karancin albashi.

A zantawar sa da manema labarai, shugaban kungiyar Joe Ajaero ya koka da yadda rayuwa ke ci gaba da yi wa ‘yan Najeriya tsada tun bayan cire tallafin man fetur da wasu manufofin kudi da gwamnatin shugaba Tinubu ta bullo da su, wanda ya ce dole ne su kalubalance su.

To ko da ya kasance an samu karin albashin zuwa naira miliyan daya, wane tasiri hakan zai haifar ga rayuwar ma’aikatan Najeriya? Tambayar da Salisu Ado yayi wa Dakta Nazifi Wada, masani kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum.

Har yanzu dai akwai jihohi a Najeriya da basu kai ga kaddamar da mafi karancin albashi na Naira dubu 30 ba.

Leave a Reply