Kungiyar Kwadago Ta NLC Ta Baiwa Majalisar Dokoki Jerin Bukatun ’Yan Najeriya

Shugaban kungiyar kwadago ta NLC Joe Ajaero, ya damka wa majalisar dokoki ta kasa kundin bukatun al’ummar Najeriya zuwa ga gwamnatin tarayya.

Bukatun da Ajaero ya damka a hannun shugaban kwamitin kwadago da samar da ayyuka na Majalisar Dattawa, Sanata Diket Plang, sun hada da aiwatar da daukacin bukatun kungiyar kan jin dadin ma’aikata da kuma samar da ayyukan yi ga ’yan kasa.

Sauran su ne gyara matatun man gwamnati guda hudu da ke kasar da kuma ba wa manoma tallafin noma ba tare da bata lokaci ba, domin saukaka samar da abinci a kasa ya kuma wadata.

Kwamred Ajaero ya shaida wa Sanata Diket Plang cewa al’ummar Najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumanar ce saboda yunwar da ke addabar su, inda ya kwatanta halin da kasar ta tsinci kanta da na kasar Zimbabwe.

A nasa bangaren, Sanata Plang ya ba su tabbacin tattauna bukatun masu zanga-zangar da nufin ganin an yi abin da ya dace.

Leave a Reply