Kungiyar Kwadago ta NLC ta baiwa gwamnati Kwana 7 Ta Soke Karin Kudin Lantarki

Kungiyar Kwadago ta NLC ta ba wa gwamnati da kamfanonin wutar lantarki wa’adin mako guda kan su soke karin kudin da suka yi a kasar. 

Shugaban NLC na Kasa, Kwamred Joe Ajaero da takwaransa na Kungiyar TUC, Fetus Osifo ne suka ba da wa’adin a jawabinsu na hadin gwiwa albarkacin zagayowar bikin ranar ma’aikata a Abuja.

Kungiyoyin sun bayyana takaicinsu bisa rashin samun tsayayyiyar wutar lantarki a Najeriya, inda suka ce hakan yana kawo mummunan koma-baya ga cigaban tattalin arzikin kasar.

Sun bayyana cewa don haka ya zama dole gwamnati ta hada hannu da al’ummar kasa wajen samar da tsarin da zai tabbatar da samuwar makamashi mai dorewa ga al’ummar Najeriya.

Shugabannin kwadagon sun jaddada cewa sama da shekara 10 da gwamnati ta cefanar wa ’yan kasuwa bangaren samar da wutar lantarki, har yanzu matsalolin bangaren sun ki ci sun ki cinyewa.

Leave a Reply