Kungiyar Kwadago ta nemi kari kan albashin naira dubu dari 615

Kungiyar ƙwadago ta Najeriya ta NLC ta ce gwamnatin tarayya ta sake gayyatan su domin komawa teburin shawara, don ganin an warware taƙadamar da bangaroirin ke yi da juna kan batun albashi mafi ƙaranci na ma’aikatan ƙasar na naira dubu dari 615.

A ranar 21 ga watan Mayu ne ake sa ran kwamitin gwamnatin tarayya zai sake tattaunawa da wakilan kungiyoyin kwadagon da suka hadar NLC da TUC bayan da wakilansu sun fice daga tattaunawar da aka yi a ranar 15 ga watan Mayu.

Kwamared Kabiru Ado Minjibir wanda shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwdagon ta NLC a Najeriya ya shaidawa BBC cewar akwai yiwuwar su nemi ƙari kan abin da suka nema a farko, kasancewar a lokacin da suka nemi kari zuwa naira dubu 615 gwamnati ba ta kara kudin wutar lantarki ba.

A tattaunawar da bangarorin biyu suka yi a baya gwamnatin tarraya ta yi wa kungiyoyin kwadagon tayin albashi dubu 48 a matsayin albashi mafi karanci yayin da kamfanoni sun yi mu su tayin naira dubu 54 abinda kuma ya sa kungiyoyin kwadagon suka fusata tare da ficewa daga dakin taron.

Leave a Reply