kungiyar jami’o’i kasa ASUU ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adi kan gazawar da aka yi na sake kafa majalisar gudanarwar jami’o’i a kasar nan

Kwanaki kadan bayan kungiyar ma’aikatan jami’o’i ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adi kan gazawar da aka yi na sake kafa majalisar gudanarwar jami’o’i a fadin kasar nan, an fitar da jerin sunayen mambobin manyan makarantu 111.
Makarantun 111 sun hada da jami’o’i, polytechnics, da kwalejojin ilimi.
Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce ana sa ran Gwamnatin Tarayya za ta maido da rusassun majalisun gwamnatocin, ba wai ta kafa wasu sabbi ba.
Osodeke ya kuma bayyana cewa, bukatar kungiyar ba wai batun rusasshiyar hukumomin manyan makarantu ba ne, ya kara da cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta aiwatar da wasu bukatu na ASUU.

Leave a Reply